ABNA24 : Wani babban jamiín soja na kasar Sudan ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarun cewa; tawagwar HKI da ta Amurka da su ka ziyarci Khartum a makon da ya wuce sun gana ne da jagoran majalisar rikon kwarya kasar Sudan, Abdulfattah Burhan da kuma manyan masu bayar da shawara ga shugaban gwamnati Abdullah Hamduk, dangane da matakai na karshe na kulla alaka da Tel Aviv.
Wani jimiín gwamnatin kasar ta Sudan na daban ya bayyana cewa: Yarjejeniya ta gaba da za a kulla ta kunshi taimako daga HKI da kuma zuba hannun jari, musamman a bangaren fasahar sadarwa da noma a cikin kasar ta Sudan.
Har ila yau, jamiinn na gwamnatin Sudan ya ce; Jamián na gwamnatin Sudan da HIK sun kuma tattauna da kasashen yankin tekun pasha, da kuma wasu na turai hanyoyin da za a yi domin zuba hannun jari a kasar Sudan, da kuma rage musu basussukan da ake bin su.
Bugu da kari majiyar ta ce; A kowance lokaci daga yanzu, shugaban kasar Amurka Donald Trump zai iya sanar da kulla alaka tsakanin HKI da Sudan.
Ana kuma sa ran cewa Sudan za ta biya Amurka diyyar kudin da suka kai dala miliyan 335 saboda harin da aka kai a ofisoshin jakadancin Amurka a Sudan da Kenya a 1998.
342/